An kashe mutane 40 a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
June 21, 2017Talla
Tashin hankalin wanda aka kwashe tsawon yinin jiya ana yi tsakanin Kiristoci na Antibala da Musulmi na Kungiyar Seleka. Ya faru ne a dai dai lokacin da aka cimma wata yarjrjenia a birnin Roma na Italiya tsakanin bangarorin 'yan tawayen da kuma gwamatin da ke yin gaba da juna wanda Cocin Roman Katolika ya shiga tsakani, don kawo karshen tashin hankalin da aka kwashe dogon lokaci ana yi a Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya