1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An halaka mayakan al-Shabaab a Kenya

Zainab Mohammed Abubakar
August 2, 2023

Kimanin mayakan al-Shabaab 60 ne jami'an tsaron Kenya suka halaka, yayin wani taho mu gama da suka yi a yankin Tana.

https://p.dw.com/p/4Uhjb
Somalia Mogadishu | Al-Shabaab Kämpfer während Militärübung
Hoto: Farah Abdi Warsameh/AP/picture alliance

Ministan cikin gida na Kenyan Kithure Kindiki ne ya bayyana hakan, inda ya ce mayakan na al-Shabaab sun kai hari a kan motocin Bus-Bus masu yawa kafin jami'an tsaron da ke sintiri su mayar da hankali.

Kindiki ya kuma nunar da cewa, fararen hula biyu sun halaka a yayin harin. A baya-bayan nan dai ana yawan samun hare-hare a yankin arewacin Kenya daga kungiyar ta al-Shabaab da ta addabi makwabciyarta Somaliya.