An kashe madugun ´yan tawayen janhuriyar Chechniya | Labarai | DW | 17.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe madugun ´yan tawayen janhuriyar Chechniya

An halaka mutumin nan da ayyana kansa shugaban jamhuriyar Chechniya Abdul-Khamid Saidulayev. A halin da ake ciki shugaban gwamnatin Chechniya Ramzan Kadyrov ya tabbatar da rahotannin da kafofin yada labarun Rasha suka bayar game da rasuwar madugun ´yan tawayen. An halaka shi ne yayin wani samame na musamman da sojojin Rasha suka kai a garin Argun dake arewa da Grozny, babban birnin Chechniya. Ya zuwa yanzu ba a ba da karin bayani ba. A cikin watan maris na shekarar da ta gabata Saidulayev ya gaji madugun ´yan tawaye Aslan Mashadov wanda hukumomin leken asirin Rasha suka halaka.