1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana binciken dan jaridar Rasha da ya mutu a Kiev

Ramatu Garba Baba
May 30, 2018

'Yan sanda a kasar Ukraine sun ce sun soma gudanar da binciken don gano wanda ke da hannun a kisan da aka yi wa wani dan jaridan Rasha a Kiev babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/2yZho
Ukraine, Kiew: Der russische Journalist Arkady Babchenko wurde erschossen
Hoto: picture-alliance/dpa/R. Krivobok

Dan jaridan mai suna Arkadi Babchenko ya tsere daga kasarsa ta asali zuwa Ukraine a sanadiyar barazanar da ya ke fuskanta don sukar gwamnatin Kremlin kan rawar da Rashan ke takawa a rikicin gabashin kasar ta Ukraine.

Babchenko ya rasu ne a ranar Talata a sanadiyar raunin da ya samu daga harbin bindiga bayan da wasu da ba a san ko su waye ba suka bude masa wuta. Ana dai ci gaba da gudanar da bincike don gano mutanen.