An kasa fara taron Yamouscouro na ƙasar Cote D`Ivoire | Labarai | DW | 28.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kasa fara taron Yamouscouro na ƙasar Cote D`Ivoire

A birnin Yamouscouro na Cote D´Ivoire, har yanzu an kasa buda taron sulhu tsakanin ɓangarori daban-daban masu gaba da a ƙasar.

Jiya ne, a ka shirya buda wannan mihimin taro ,irin sa,na farko tun ɓarkewar rikicin tawaye a ƙasar.

Taron zai haɗa shugaba Lauran Bagbo, da Praminista Charles Konnan Banny, da madugun yan adawa Allasan Watara, da na yan tawaye Guillaume Sorro, da sauran shugabanin siyasa na ƙasa.

An ɗage taron na jiya, dalilin ƙin halartar Guillaume Sorro,

saboda ƙarancin matakan tsaro.

Wani mai magana da yawun shugaban ƙasa ya ce, za a buɗa taron a yau talata, bayan an cimma daidaito a kan matakan tsaron,

To saidai har ya zuwa yanzu ba a fara wannan taro ba.

Cemma, masharahanta sun ce ,sun san a rina, ta la´akari da yada, so da dama an sha buƙatar kiran irin wannan taro, amma a ka ƙasa cimma nasara.