An kasa cimma matsaya a taron komitin sulhu akan Iran | Labarai | DW | 21.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kasa cimma matsaya a taron komitin sulhu akan Iran

Taron manyan jamian diplomasiya a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York,ya gagara samun nasarar magance rikici akan ko wane mataki zaa dauka akan kasar Iran game da shirinta na nukiliya.

Jamiai a taron ,wanda ya hada zaunannun membobi 5 na komitin sulhu na majalisar,wato kasashen Amurka,Rasha,Sin,Burtaniya da Faransa da kuma kasar Jamus,sunce taron zai ci gaba.

Wadannan kasashe dai suna kokari ne su cimma yarjejeniya akan mataki da zasu dauka na shawo kann kasar Iran ta dakatar da shirinta na sarrafa makamashin nukiliya.

Amurka da Kungiyar Taraiyar Turai sun baiyana tsoron cewa Iran tana kera makaman nukiliya ne,Iran kuma tace shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne.