1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kara samun yawan wadanda suka rasa rayukansu a yamutsi na Makka

January 12, 2006
https://p.dw.com/p/BvCZ

Ya zuwa yanzu akalla mutane 345 ne aka bada rahoton sun rasa rayukansu cikin turmutsutsu a Makka,a rana ta karshe ta aikin hajjin bana.

Maaikatar harkokin cikin gida ta Saudiya tace mutane 289 kuma sun samu rauni cikin wannan hargitsi,daya wakana a lokacinda dubun dubatar mahajjata suka taru wajen jamra domin jifan shedan. Ministan kula da lafiya na Saudiya Hamad bin Abdallah Al maneh,ya fadawa manema labarai cewa wasu alhazai ne wadanda basu san ya kamata ba da kuma yawan kaya suka haddasa wannan yamutsi.

Shugaban masu kula da aiyukan ceto na birnin Makka Khaled Yasin ya fadawa AFP cewa sun, tura motocin ambulance 70 zuwa jamra da kuma cibiyoyin kula da lafiya 7 na Makka domin kula da wadanda suka samu rauni,yace ba zai yiwu a dauko masu raunin da jirage masu saukar angulu ba saboda cunkoson jammaa.

A lokutan aikin hajji a baya an samu turmutsutsu irin wannan inda a shekarar 1990 mutane fiye da1,400 suka rasa rayukansu.