1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An kammalla taron AU a Addis Ababa

Shugabanin ƙasashen AU sun rufe taro karo na 8 a birnin Addis Abeba na ƙasar Ethiopia

default

Shugabanin ƙasashe da na gwamnatocin ƙungiyar gamayya Afrika, sun kammalla zaman taron yini 2, a birnin Addis Ababa na ƙasar Ethiopia.

Taron, wanda shine karo na 8 da ya haɗa shugabanin Afrika, ya tantana batutuwa da dama, da su ka jiɓanci kokowa da gursuwar Hamada, da kuma kimiya da Fasaha a nahiyar Afrika.

Saidai mahimman batutuwan da su kafi mamaye mafi yawan tebrorin mahaurorin mahalarta wannan taro, sune na yaƙe yaƙe da ke ci gaba da wakana a Sudan da Somalia.

A lokacin da ya gabatar da jawabin rufe taro, saban shugaban ƙungiyar gamayar Afrika John kufor, yayi kira da babbar murya, ga shugabanin Afrika, su yi wa Allah da annabin sa ,su taimaka da sojoji, da kuma kuɗaɗe,domin magance fitinar da ta ɓarke a Somalia.

Shugaban ya ce, a halin yanzu, an samu sojoji dubu 4 kaɗai, daga jimmilar dubu 8, da komitin tsaron ƙungiyar AU ke buƙatar aikawa a Somalia.

Ya zuwa yanzu kuma, ƙasashwe 5 kyak ! su ka bayyana anaiyar tura dakarun su.

Saidai wata babbar nasara da aka cimma, itace amincewar da shugaban ƙasar Somalia, Abdullahi Yusuf Ahmed,yayi ta hawa tebrin shawara tare da yan tawayen kotunan Islama,inda har ma, ya alƙawarta kiran babban taron haɗin kan ƙasa.

Ƙungiyar AU, da ƙungiyar Gamayya turai, sun yaba da wannan mataki, kamar yada komishinan ci gaba na EU Louis Michel ya bayyana a wajen taron:

„Mun fahinci juna, da Gwamnatin Somalia, domin a yanzu mu na magana da murya ɗaya.

Samar da zaman lahia mai ɗorewa a Somalia, daidai yake, da cimma matakin sulhu a dukkan ariyar ƙafon Afrika.

Sannan, mun yi farin ciki, da matakin da shugaban ƙasar Somalia ya ɗauka, na tantanawa da dakarun Islama don warware rikicin cikin ruwan sanhi“.

A dangane da rikicin yankin Darfur na ƙasar Sudan, a nan ma, taron ƙungiyar gamayya Afrika, ya yi nasara ciwo kan shugaban Omar El-Beshir na Sudan, ya amince da karɓar tawagar dakarun Majalisar Ɗinkin Dunia.

Shugabanin ƙasashe da na gwamnatocin Afrika za su zaman taro na gaba, a watan juli na wannan shekara, a birnin Accra na ƙasar Ghana.

 • Kwanan wata 31.01.2007
 • Mawallafi Yahouza S Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtwS
 • Kwanan wata 31.01.2007
 • Mawallafi Yahouza S Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtwS