An kammalla tantanawa tsakanin tawagar Tabon Mbeki da tawagogin Cote D´Ivoire | Labarai | DW | 02.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammalla tantanawa tsakanin tawagar Tabon Mbeki da tawagogin Cote D´Ivoire

A kasar Cote D´Ivoire, an kamala tantanawar kwanaki 2, tsakanin tawagar shugaba Tabon Mbeki na Afrika ta kusdu, mai shiga tsakanin rikicin kasar, da bangarorin daban daban masu gaba da juna.

Saidai kamar yadda masu hasashen al´ummara su ka tsinkayo, wannan tatannawa ba ta cimma wani abin azo a gani ba.

Mahimman batutuwan da su ka maida himma akai, sun hada da na majalisar dokoki, da wa´adin ta ya kai karshe, da kuma zabuka daban daban ,da za a shirya a cikin wannan shekara.

Yan tawayen FN da ke rike da arewancin kasar sun kauracewa tantanawar.

Kazalika, madugun yan adawa Alasan watara, da ya dawo satin da ya gabata daga gudun hijira, ya bayana kin amincewa da ci gaban wa´adin majalisar dokoki , sabanin shugaban Lauran Bagbo.

A nasa bangare, sakatare jannar na Majalisar Dinkin Dunia Koffi Annan ,ya yi kira ga hukumomin Cote D´Ivoire, da sauran bangarori da ke fada aji a wannan kasa da su tabbatar da sun kare lafiyar ma´aikatan majalisar dinkin dunia da ke hidima a kasar.