1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala zaben shugaban kasa a Srilanka

November 17, 2005
https://p.dw.com/p/BvKg

A dazu dazun nan ne aka rufe tashohin zabe na shugaban kasa da aka gudanar a yau a can kasar Srilanka.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa da yawa daga cikin wadanda suka cancanci yin zabe a gabashin kasar basu fito ba don kada kuriun nasu a lokacin wannan zabe, to sai dai a wasu yankunan da yawa daga cikin masu zaben sun fito sun kuma kada kuri´un nasu.

Fuskantar hakan kuwa a cewar bayanai nada nasaba da kauracewa zaben da mabiya kungiyyar Timil Tigers suka yi.

Ba a da bayan haka kuwa, rahotannin sun shaidar da cewa an fuskanci yan rigingimu, wanda hakan yayi sanadiyyar rasuwarr mutane biyu, wasu kuma sha bakwai suka jikkata.

A cewar jami´ai masu sa ido daga kasashen ketare, wannan zabe na kasar ta Srilanka ya zamo na farko a yan shekarun nan da aka gudanar ba tare da fuskantar tashe tashen hankula mafi muni ba.

Ana dai sa ran fitowar cikakken sakamakon wannan zabe a gobe juma´a idan Allah ya kaimu.