1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala zaben raba gardama a Algeria

ibrahim SaniSeptember 30, 2005

Zabe mafi tarihi na raba gardama a Algerii ya kammala, abin da ya rage yanzu shine a fara aiwatar da abubuwan dake cikin wannan kuduri da aka amincewar

https://p.dw.com/p/BvZI
Hoto: AP

Da gagarumin rinjaye alummar kasar ta Algeria sun kada kuriar amincewa da wannan sabon daftari na zaman lafiya da aka gabatar musu.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa kuriar raba gardamar a yanzu haka na a matsayin wani gagarumin yunkuri take na kawo karshen yakin basasa da kasar tayi fama dashi shekara da shekaru.

A dai tsawon wannan lokaci an kiyasta cewa mutane sama da dubu dari ne suka rasa rayukan su daga bangarori daban daban na kasar.

Bayanai dai daga kasar a yanzu haka na nuni da cewa wannan kuriar raba gardamar da a can baya ta sha fuskantar suka,an kiyasta cewa kashi tamanin na alummar kasar kusan miliyan 18 ne suka amince da wannan daftari na zaman lafiyar.

Wannan daftari na zaman lafiyar a yanzu haka zai yiwa kusan mabiya addinin islama na kasar yan tawaye da suka fafata a lokacin wannan mawuyacin hali da kasar ta fada a ciki ahuwa.

Da yawa dai daga cikin ire iren wadan nan yan tawaye sun kasance sanadiyyar rasa rayukan da kasar tayi na kusan mutane sama da dubu dari daya a tsawon wannan lokaci da akayi ana fafatawa.

Wannan dai kuriar raba gardama da aka gudanar a jiya alhamis a cewar ministan harkokin wajen kasar wato Nuruddin Zarhouni, na a matsayin wani gagarumin abin tarihi ne ga Alummar kasar ta Algeria.

Ministan harkokin wajen kasar yaci gaba da cewa irin yadda alummar kasar suka fito kwansu da kwarkwata wajen wannan zabe ya nuna a fili irin yadda Alummar kasar suka marawa wannan shiri na shugaba Abdelaziz Bouteflika baya.

Kamfanin dillancin labaru na Reuters ya rawaito wani dan kasar mai suna Slimane azi dake sana´ar makanike na cewa ya jefa kuriar sane ta amincewa da wannan shiri domin a cewar sa babu abin da yafi zaman lafiya da juna.

Duk da cewa an amince da gagarumin rinjaye game da wannan shiri,a waje daya kuma an fuskanci wasu yan tashe tashen hankula musanmamma a yankin Kabylie, inda yan adawa suka bukaci alumman su dasu kauracewa wannan zaben na raba gardama.

Ata bakin daya daga cikin mai gudun hijira na yankin wato Hocine Ait Ahmed, cewa yayi wannan shiri na zaman lafiyar wani yunkuri ne daga bangaren shugaban kasar na kokarin cimma burin sa na yin tazarce a gadon mulkin kasar.

Dan gudun hijirar yaci gaba da cewa babu masu sa ido na kasashen ketare da suka ganewa idon su yadda wannan zabe ya gudana, sannan a hannu daya kuma ga yadda masu nazarin siyasa na kasa da kasa ke fadi na cewa akwai yar zagalin zagalin a cikin sakamakon wannan zabe.

Kafin dai cimma wannan mataki, bayanai daga kasar sun nunar da cewa kasar ta Algeria na a cikin wani matsanancin hali ne na rashin kyakkyawan tsaro sakamakon irin balahirar dake wanzuwa a tsakanin jamian tsaro da kuma masu tsattsauran raayin yan tawaye mabiya addinin islama.

Sai dai kuma a waje daya, kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya sun bayyana korafin su da cewa, shugaban kasar ta Algeria ya sako wannan tsarin yin ahuwar ne bisa wani yunkuri na dauke hankalin duniya don ya wanke irin taasar da ire iren wadan nan yan tawayen suka aikata a tsawon wannan lokaci.