An kammala zabe na gama gari a Iraq | Labarai | DW | 15.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala zabe na gama gari a Iraq

Wasu jami´an yan sanda na Iraq i da yawan su ya tasamma zambar dubu biyu sun koka game da damar da ba a basu ba na kada kuriun su a lokacin zaben gama gari daya gudana a yau.

Jami´an yan sandan sun mika wannan koken nasu ne kuwa ga ma´aikatar kula da al´amurran cikin gida ta kasar.

A cewar majiya mai karfi, jamian yan sandan da suka kada kuriun nasu a yau, yan sanda ne dake gadin tashohin zabe da suka nuna takardar shaidar dan kasa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa tashe tashen hankulan da aka fuskanta a lokacin zabebn na yau , bai hana wadanda suka can can ci yin zaben fitowa don kada kuriun nasu ba.

Masu zaben dai sun kada kuriun nasu ne don zabar kujerun yan majalisu 275.

Bayanai dai sun nunar da cewa da yawa daga cikin mabiya darikar sunni sunyi ba zata wajen fitowa da yawan gaske don kada kuriun nasu , sabanin kauracewa hakan da suka yi a zaben watan Janairu daya gabata.

Ya zuwa yanzu dai ana hasashen cewa gamayyar jamiyyun darikar shi´a ne zasu lashe wadan nan kujeru da gagarumin rinjaye.