An kammala zaɓen shugaban ƙasa da na yan majalisun dokoki a RDC | Labarai | DW | 30.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala zaɓen shugaban ƙasa da na yan majalisun dokoki a RDC

A Jamhuriya Demokaradiyar Kongo, an kammalla zaɓen shugaban ƙasa da na yan majalisun dokoki da ka gudanar yau, a fadin ƙasar baki ɗaya.

A jimilce zaɓen ya wakana lami lafia, in banda yan matsaloli na da cen, wanda ba masu tada hankali ba.

Kasar Belgium da ta yi wa Jamhuriya Demokradiyar Kongo mulkin mallaka, ta bayana gamsuwa da yadda zabukan su ka gudana cikin tsari da sannin ta kamata.

Za a fara ƙidayar ƙuri´u a runfunan zaɓe dubu 50 tun daga daren yau.

Nan da makwani 3 masu zuwa, a ke sa ran samar da sakamakon zagaye na farko.

Rahotani daga sassa daban-daban na ƙasar sun ce mutane sun hito da himma a runfunan zaɓe.