An kammala zaɓen shugaban ƙasa a Thailand | Labarai | DW | 02.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala zaɓen shugaban ƙasa a Thailand

An kamalla zaɓen yan majalisun dokoki, da a ka gudanar yau, a ƙasar Thailand.

Saidai wannan zaɓe, ya fuskanci tashe tashen hankulla, a yayin da yan ƙunar baƙin wake, su ka kai hare haren bama bamai, a wasu yakunan ƙasar.

Mutane 9, su ka ji raunuka, da su ka haɗa da jami´an tsaro 6.

A yankunan da musulmi su ka fi rinjaye, rahotani sun bayyana cewar, jama´a, ta fito da himma , a runfunahn zaɓe,saidai sun zaɓi fara kati,mai shaida cewa, basu amince ba, da ko wane ɗan takara.

Sunyi hakan, domin nuna rashin amincewar su, da tafiyar harakokin siyasar ƙasar.

Fiye da mutane million 45, ya cencenta su kaɗa kuri´u, a runfuna zaɓe dubu 87.

Saidai, mayan jam´iyun adawa, sun yanke shawara ƙin halartar zaɓen, wanda a ka shirya shekaru 3, kamin lokacin sa , dalili da zanga zangar, da al´ummar ƙasar ke ci gaba da yi, domin nuna ƙin jinnin Praminista Thaksin Shinawatra.

An zaɓi Praministan, a shekara ta 2001, ya kuma yi tazarce, a zaɓen da a ka shirya , watani 18 kacal, da su ka wuce.

A wannan karro , yayi alkawarin tsame hannuwan sa, kwata kwata,daga harakokin siyasa, muddun bai samu kashi 50 bisa 100 ba, na yawan ƙuri´un da a ka jefa a zaɓen na yau.