An kammala taron tattalin arzikin duniya a Cape Town | Labarai | DW | 02.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala taron tattalin arzikin duniya a Cape Town

Tare da nuna kyakkyawan fatan samun bunkasar tattalin arzikin nahiyar Afirka, an kammala wani babban taro game da tattalin arzikin duniya a birnin Cape Town na kasar ATK. Sabon shugaban Tanzania Jakaya Kiwete ya yi kira da kasashen Afirka da su koyi da kasashen China da Indiya wadanda ke samun bunkasar tattalin arziki a yanzu. A jawabin da yayi a gun taron shugaba Kiwete ya ce a halin da ake ciki kasashen biyu na kara nuna sha´awar zuba jari a nahiyar Afirka. A wajen taron dai an bude wani asusu na dala miliyan 100, wanda za´a yi amfani da shi wajen wanke sunan Afirka musamman game da zuba jari a wannan nahiya.