1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala taron Merkel da Blair a London

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tace kyautata dangantaka a tsakanin kasar ta da kasashen Faransa da Biritaniya na daya daga cikin abubuwan da gwamnatin ta zata fi mayar da hankali a kai.

Bugu da kari sabuwar shugabar Jamusawan taci gaba da cewa samun cikakken hadin kai a tsakanin kasashen Biritaniya da Faransa shine zai kawo warwarewar al´amurra a game da sabanin da aka fuskanta dangane da kasafin kudi na kungiyyar EU.

A wani taron manema labarai da Merkel ta gudanar tare da Blair a birnin London, taki ta fito fili ta nuna kasar da tage goyon baya a tsakanin wadan nan kasashe biyu. A maimakon hakan Angela Merkel taci gaba da bada amsa da cewa babu abin da tasa a gaba illa ganin an samu nasarar shawo kann sabanin da aka fuskanta.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa a tattaunawar da shugabannin biyu suka yi a yau,sun mayar da hankalin sune kacokan wajen batun daya shafi kasafin kundin na kungiyyar ta EU.

Kafin dai zuwan ta kasar ta Biritaniya a jiya ,Angela Merkel ta kai irin wannan ziyara izuwa kasar Faransa a inda ta sadu da shugaba Jack Chirac