1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala taron Lebanon a Rom ba tare da cimma yarjejeniya ba

July 26, 2006
https://p.dw.com/p/Bup1
Mahalarta babban taron birnin Rome akan rikicin kasar Lebanon sun kasa cimma yarjejeniya akan ka´idojin tsagaita wuta don kawo karshen fada tsakanin Isra´ila da ´yan yakin sunkurun Hisbollah. To sai dai gwamnatin Libanon da manyan jami´an harkokin ketare daga Amirka, yankin GTT da nahiyar Turai sun amince akan bukatar girke dakarun kasa da kasa a karkashin inuwar MDD a yankin kudancin Lebanon. Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta yi kira da a kawo karshen mummunan fadan, to amma ta ce ba za´a koma gidan jiya ba na rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a Libanon. Shi ma FM Libanon Fuad Siniora yayiwa taron jawabi inda ya nuna muhimmancin cimma wani shirin tsagaita bude wuta.