An kammala taron kungiyar opec a Vienna | Siyasa | DW | 16.09.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An kammala taron kungiyar opec a Vienna

Farashin man fetur a kasuwannin duniya na cigaba da tashin gwauran zabi duk kuwa matakin da kungiyar opec ke dauka

default

A kokarin da kungiyar opec keyi na tabbatarwa kasashen duniya cewa zata iya daidaita farashin man fetur a kasuwannin duniya ta amince da karin hako gangar man fetur da kusan miliyan daya a kowace rana daga kasashen dake cikin kungiyar ta opec a halin yanzu .Bugu da kari kungiyar dai na tuntubar sauran kasashen dake da man fetur wadanda basa cikin kungiyar dasu bi sahun kungiyar domin cimma manufar da aka sanya a gaba ..Toron daya amince da karin kusan kaso 4 cikin dari na adadin man da ake hakowa a jiya laraba har kawo yanzu wakilan kungiyar na cigaba da wani taro na musamman daga yau zuwa gobe jummaa ..A ranar 27 ga watan nuwamba dai kungiyar ta amince da karin man fetur a kasuwannin duniya ga kasashen dake cikin kungiyar da kimanin ganga sama da miliyan 27 a kowace rana ..A dangane da haka dai wakilan sun cimma daidaito cewa duk da wannan matakin da kungiyar zata dauka a nan gaba da wuya a cimma manufa daya na daidaita sahu ta wannan fannin ..Ministan harkokin man fetur na kAsar Algeria dai ya tabbatar da cewa ga dukkan alamu hakan ka iya samar da waraka a dangane da farashin a kasuwannin duniya ..To sai dai a yau dai kowace gangar man fetur akan sayar da ita dAla 45 a kasuwannin duniya wanda hakan ke cigaba da nunin cewa farashin na cigaba da fuskantar tashin gwauran zabi Wata majiya dai na cewa duk da matakin da kungiyar ta dauka na samar da karin ganga miliyan daya a kowace rana ya gaza sauko da farashin a kasuwannin duniya a halin yanzu .A daura da haka dai shugaban kungiyar ta opec a halin yanzu wakilin kasar Indonesiya ya tabbatar da cewa a nan gaba kadan farashin zai sauko domin samun waraka a kasuwa .kasar Rasha wacce ta kasance bata cikin kungiyar ta opec bata bayar da wani batu mai karfi ba a dangane da wannan bukatar da kungiyar ta opec ta bukata .A hannu guda dai kasar saudiyya tace zata hako kimanin ganga miliyan daya da dubu dari biyar a kowace rana domin kari ga gangar mai da ake hakowa bisa amincewar kumngiyar ta opec .Tun ba yanzu ba dai kungiyaer take nem,an samun daidaito kann farashin man fetur din ga dala 22 zuwa 28 a kowace ganga amma har kawo yanzu hakan ya gaza cimma ruwa .To sai dai kungiyar a watan disamba na wannan shekara zata gudanar da wani taro a can kasar masar kann wannan batun A bisa farashin man fetur din dai a kasuwannin duniya Amuerka ta gigita a sabili da cewa tafi kowace kasa anfani da wannan sinadari wanda take faman kaiwa da komowa domin sauko da farashin yarda ya dace .Idan allah ya kaimu dai kungiyar ta opec tace baya ga taron kasar Masar za kuma ta gabatar da wani a can Kasar Iran a WataN Maris din shekara ta 2005 kann daidaita farashin a kasuwanni .