An kammala taron kungiyar EU ba tare da cimma wata yarjejeniya ba | Labarai | DW | 16.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala taron kungiyar EU ba tare da cimma wata yarjejeniya ba

An kammala taron kolin yini biyu na KTT ba tare da cimma daidaito ba game da daftarin kundin tsarin mulkin kungiyar ta EU. To sai dai an amince da tsayar da shawara ta karshe dangane da kundin tsarin mulkin wanda kasashen Farasna da NL su ka yi watsi da shi, a juzu´i na biyu na shekara ta 2008. Wani tsarin lokaci da aka amince da shi a gun taron kolin ya tanadi cewar ya kamata Jamus wadda zata karbi ragamar shugabancin EU a juzu´in farko na shekara ta 2007, ta dauki sabbin matakai da nufin farfado da shirye-shiryen amincewa da kundin tsarin mulkin. A dai tsawon wannan lokaci na dakatar da kundin tsarin mulkin, EU zata mayar da hankali akan batutuwan da suka shafi samar da aikin yi, ba da ilimi mai nagarta sai kuma yaki da bakin haure a cikin kasashen kngiyar. Duk da wannan saiko shugaban hukumar zartaswar EU Jose Manuel Barroso ya yi kyakkyawan fatan cewa za´a kai gaci.