An kammala taron kolin shugabannin kungiyar EU da na Latun Amirka | Labarai | DW | 12.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala taron kolin shugabannin kungiyar EU da na Latun Amirka

An kammala taron koli tsakanin shugabannin kasashen Turai da takwarorinsu na yankinLatun Amirka a birnin Vienna. Kasashen KTT da kuma da yawa daga cikin kawayensu na yankin Latunamirka sun yi tir da shirin gwamnatin Bolivia na mayar da kamfanonin ketare mallakinta da cewa gurgun mataki ne a yakin da ake yi da talauci. A gun taron kolin shugabannin kungiyar EU da takwarorinsu na Latunamirka da aka kammala dazu dazun nan a birnin Viennan kasar Austria an yi watsi da manufofin shugaban Venezuella Hugo Chaves da takwaransa na Bolivia Evo Morales. Sanarwar bayan taron da aka bayar, shugabanni 62 da suka halarci taron kolin suna nuna aniyar su ta karfafa ba juna hadin kai a batutuwa da dama ciki har da na ba da taimakon raya kasa da kare hakkin ´yan Adam, kare muhalli da kuma yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi.