1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala taron kolin kungiyar D-8 a tsibirin Bali

Taron kolin kungiyar D-8 ta kasashe masu tasowa wadanda musulmi suka fi rinjaye a cikin su, bai tattauna kai tsaye game da takaddamar da ake yi akan shirin nukiliyar Iran ba. Shugaban Indonesia Susilo Bambang Yudhoyono ya bayyana haka a wani taron manema labarai a karshen taron kungiyar ta D-8 da ya gudana a tsibirin Bali na kasar ta Indonesia. Mahalarta taron kolin sun tattauna akan batutuwan da suka hada da hauhawar farashin mai a duniya da dangantaka tsakanin musulmi da sauran kasashen duniya. Shugaban Indonesia wanda ya karbi ragamar shugabancin kungiyar daga shugaba Mahmud Ahmedi Nijad na Iran, yayi kira da a samar da kyakkyawan yanayin tuntubar juna tsakanin mabiya addinai da kuma al´adu dabam-dabam. Kungiyar ta D-8 ta kunshi kasashen Bangladesh, Masar, Indonesia, Iran, Malaysia, Nigeria, Pakistan da kuma Turkiya.