1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AN KAMMALA TARON KOLI NA RUKUNIN KASASHEN APEC

YAHAYA AHMEDNovember 22, 2004

Shugabannin kasashen rukunin APEC sun kammala taron kolinsu na yini biyu a birnin Santiago de Chile, a karshen wannan makon. Gurin taron taron ne dai tattauna hanyoyin inganta cinikayya a kasuwannnin duniya. Amma shugaba Bush na Amirka, wanda shi ma ya halarci taron, ya yunkuri yi wa ajandar tattaunawar babakere, da manufofinsa na angaza wa Iran da Korea Ta Arewa su kau dda shirye-shiryensu na mallakarr makamashin nukiliya.

https://p.dw.com/p/BveS
Shugabannin kasashen rukunin APEC cikin wasu rigunan gargajiya na kasar Chile, a taron kolin da suka halarci a birnin Santiago.
Shugabannin kasashen rukunin APEC cikin wasu rigunan gargajiya na kasar Chile, a taron kolin da suka halarci a birnin Santiago.Hoto: AP

A karshen taron koli na yini biyu da suka yi a Santiago de Chile, babban birnin kasar Chile da ke Amirka Ta Kudu, shugabannin kasashen rukunin nan na APEC, wanda ya kunshi kasashen yankin Pacific, sun kuduri aniyar daukar ingantattun matakan tsaro, don kare hada-hadar ciniki na kasa da kasa. Daya daga cikin matakan kuwa, shi ne ba da kaimi wajen yakan ta’addanci.

Duk shugabannin dai, sun yarje kan daukan tsauraran matakan tsaro a fannin sufurin jirgin sama da kuma na jiragen ruwa, don hana `yan ta’adda kai musu farmaki. Har ila yau dai, sun kuma karfafa cewa za su iza wuta a yaki da cin hanci da rashawa.

A huskar harkokin cinikayya na kasa dda kasa kuma, kasashen rukunin na APEC sun nuna goyon bayansu ga yunkurin da ake yi na kau da shingaye a kasuwannnin duniya. Ministocin ciniki da na harkokin waje na kasashen ne suka yarje kan haka a ganawar da su ka yi a birnin na Santiago. Sun kuma nuna cikakken goyon bayansu ga ci gaba da tattaunawar kungiyar ciniki ta duniya, da ake tafiyar hawainiya a kanta a halin yanzu.

Rukunin na APEC dai ya kuma dau alkawarin tallafa wa mambobinsa guda biyu, wato Rasha da Vietnam, a yunkurin da suke yi na samun karbuwa a Kungiyar Ciniki ta Duniya.

A nasa bangaren, shugaban Amirka, George W. Bush, ya fi mai da hankalinsa ne wajen neman goyon bayan kasashen APEC din, ga manufarsa ta angaza wa Korea Ta Arewa, a rikicin da kasashen biyu ke yi kan shirin mallakar makamashin nukiliya da Korea Ta Arewan ta sanya a gaba. Shugaba Bush dai ya fito kiri-kiri a gun taron, ya bukaci shugaba Kim Jong Il na Korea Ta Arewa da ya soke wannan shirin. Bayan ganawar da ya yi da shugabannin kasashen Japan, da Sin, da Rasha, da Korea Ta Arewa, da Kyanada da Indonesia, shugaba Bush ya nanata cewa, Korea Ta Arewa na gefe daya ne ita kadai, gaban duk duniya da suka hada kai wajen nuna adawarsu ga manufarta.

Game da Iran kuma, shugaba Bush ya zargi mahukuntan birnin Teheran, da ci gaba da sarrafa wata gas mai suna Urenium Hexaflluorid, wadda guba ce, wadda kuma za a iya yin amfani da ita wajen hada makaman kare dangi. Ita dai Iran ta ba da sanarwar cewa, tun daga yau litinin ne, za ta fara aiki da wata yarjejeniyar da ta cim ma da kasashen Turai guda 3, wato Birtaniya, da Faransa da Jamus, ta tsai da duk wasu ayyukan azurta sinadarin Yurenium a kafofin makamashinta. Amma jami’an Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta kasa da kasa da ke da cibiyarta a birnin Vienna, sun ce Iran na amfani da sauran dan lokacin da ya rage mata kafin yarjejeniyar ta fara aiki ne, wajen sarrafa dimbin yawan wannan gas mai guba.

A birnin na Santiago de Chile dai, dubban mutane sun yi zanga-zangar nuna adawa ga bayyanar shugaba Bush a taron da kuma nuna rashin amincewarsu, ga yakar kasar Iraqi da yake ta yi har ila yau. A ran juma’a kawai, `yan sandan birnin sun ce, fiye da mutane dubu 25 ne suka shiga zanga—zangar. Masu zanga-zangar dai sun yi fito na fito da `yan sanda, wadanda suka yi ta harba musu barkonon tsohuwa don su tarwatsa su.

K

asashen da ke cikin rukunin na APEC suun hada ne da Amirka, da Rasha, da Kyanada, da Japan, da Sin, da Austreliya, da New Zealand, da kasashen kudancin Amirka na Chile, da Peru da Mexiko, da kuma mafi yawan kasashen Kudu Maso Gabashin Asiya.