1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala taron kasashen Afrika da Sin

November 5, 2006
https://p.dw.com/p/BudH

Shugabannin kasashen Afrika dana kasar Sin sun baiyana bukatunsu na karfafa hadin kai tare da bullo da sabbin dangantaku tsakaninsu.

Hakazalika shugabannin sunyi alkawarin kara girman harkokin kasuwanci zuwa dala biliyan 100 daga nan zuwa shekara 2010.

Sunyi wannan alkawari ne kuwa a karshen taronsu da suka gudanar a birnin Beijing na kasar Sin.

Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya baiyana cewa taron wanda shugabanin kasashen Afrika fiye da 40 suka halarta da cewa taro ne mai cike da tarihi.

Kanfanonin kasar Sin da gwamnatocin Afrika da kanfanoninsu sun sanya hannu kann yarjejeniyoyin kasuwanci 14 da kudinsu ya kai dala biliyan guda da digo 9.

Kasar Sin tunda farko tayi alkawarin kara taimako da take baiwa ci gaban Afrika,haka kuma ta baiyana bude asusun dala biliyan 5 don bada rance ga kasashen Afrika.