1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AN KAMMALA TARON JAM'IYYAR GREENS A BIRNIN DRESDEN.

Yahaya AhmedDecember 1, 2003
https://p.dw.com/p/BvnJ

A taron da `yan jam'iyyar suka yi a birnin Dresden, jawabin da ministan harkokin waje Joschka Fischer ya yi musu ne, ya fi gamsad da su. Shi dai Fischer ya yi kira ne ga mambobin jam'iyyar da su goyi bayan fafutukar da Turkiyya ke yi na shiga cikin kungiyar Hadin Kan Turai. A zahiri, Fischer bai halarci taron a birnin Dresden ba. Ya yi wa mahalartan jawabi ne kai tsaye a talabijin daga birnin Naples na kasar Italiya, inda yake halartar wani taro daban kuma, na ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar Hadin KanTurai. Amma da yafara jawabinsa sai duk mahalarta 840 da ke cikin zauren taron a Dresden suka tashi suna yi masa tabi, kamar ya shigo ne cikin zauren ne da kansa. An dai yi muhawara kan batutuwa daban-daban da suka shafi garambawul din da gwamnatin tarayya ke niyyar yi wa manufofin siyasarta. A daura da taron da jam'iyyar SPD ta yi a kwanakin baya, a wannan taron na jam'iyyar Greens, ba a sami wani rashin jituwa tsakanin mambobinta ba. Mahalarta taron ba su nuna damuwarsu ga matakan tsimin da gwamnati ke dauka a halin yanzu ba, duk da sanin cewa, hakan bai dace sosai da manufofin jam'iyyarsu ba. Amma sun fahimci cewa, gwamnatin ba ta da wani zabi, sai daukan wannan matakin, idan aka yi la'akari da halin da tattalin arzikin Jamus ke ciki a halin yanzu. daya daga cikin jigogin da jam'iyyar ta fi mai da hankalinta a kai a taron na Dresden, shi ne kan batun siyasar nahiyar Turai. A nan dai, `yan Greens din, na son su jagoranci shigad da wani sauyi ne a harkokin siyasar nahiyar. Sun juya wa ra'ayin kishin kasa baya, sun fi gwammacewa su rungumi manufar cim ma hadin Kan Turai da fadada kungiyar ta EU. Sabili da haka ne kuwa, suka nemi hadin kan duk jam'iyyun Greens 22, wato masu fafutukar kare kewayen bil'adama a nan Turai, don su shiga takarar zaben majalisar Turan da za a yi a cikin shekarar badi da manufa daya.

A huskar siyasar cikin gida kuwa, `yan jam'iyyar Greens na ganin cewa, garanbawul din da gwamnatin tarayya ke yi wa kafofin kwadago da na haraji ba sa nuna adalci ga mafi yawan jama'a, musamman ma dai ma'aikata. Sabili da hakan ne kuwa, suka zartad da kudurin kara wa masu hali haraji don rage wa ma'aikata irin matsin da suke huskanta, sakamakon matakan tsimin da gwamnati ta dauka. Sai dai bisa dukkan alamu, wannan manufar da jam'iyyar Greens ta gabatar ba za ta sami karbuwa ba a majalisar dattijai. Ko da an zartad kuduri a majalisar dokoki ta taryya, sai wannan kudurin ya sami amincewar `yan majalisar dattijan da rinjayi, kafin ya zamo doka. A halin yanzu kuwa, `yan adawa ne ke da rinjayi a majalisar dattijan. Su kam tun da ma can ba su nuna sha'awwar goyon bayan matakan da gwamnatin ke dauka ba. Idan ko aka kawo wannan shawarar gabansu, babu shakka shure ta za su yi. Har ila yau akwai wasu kudurorin da ba su sami shiga ba tukuna a majalisun na tarayya, saboda jayayyar da jam'iyyun gwamnati da na adawa ke yi a kansu. A tsakiyar wannan watan ne dai, wani kwamitin sasantawar da aka kafa, zai yi kokarin cim ma wata madafa, wadda ake sa ran bangarorin biyu za su amince da ita. Tattaunawar da aka yi a birnin Dresden wata gagarumar nasara ce, saboda mahalarta taron sun sanya alamu na alkiblar da siyasar cikin gida da kuma na Turai za su mai da hankullansu a kai nan gaba, kamar yadda shugaban jam'iyyar Reinhard Bütikofer ya bayyanar, a cikin jawabinsa na rufe taron.