1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala taron ƙoli na ƙasashen rukunin G-8.

YAHAYA AHMEDJuly 17, 2006

Rikicin da ke ta ta'azzara a yankin Gabas Ta Tsakiya, shi ya dabaibaye ajandar taron ƙoli na rukunin ƙasashen G-8, mafi arzikin masana'antu a duniya, wanda aka kammala a birnin St.-Petersburg a ran lahadin da ta wuce.

https://p.dw.com/p/Btz7
Shugabannin ƙasashen rukunin G-8 a birnin St.-Petersburg.
Shugabannin ƙasashen rukunin G-8 a birnin St.-Petersburg.Hoto: AP

Bisa al’ada dai, duk ƙasar da za ta karɓi baƙwancin taron ƙoli na ƙasashen rukunin G-8, ita ke tsara jigogin da za a tatauna a kansu da kuma jera su bisa muhimmancin da take ba su. Amma a cikin ’yan shekarun da suka wuce, kusan duk tarukan ba su wakana kamar yadda masu karɓar baƙwancinsu suka tanadi shirya su ba. Ko dai wasu al’muran harkokin siyasar duniya ke dabaibaye su, ko kuma mafi yawan mahalarta taron, ba sa zama har ƙarshensa.

A lal misali, a taron ƙolin rukunin G-8 ɗin da aka gudanar a garin Evian a Faransa a shekara ta 2003, shugaba Bush na Amirka ya yi wa tsarin shirye-shiryen mai karɓar baƙwancin, wato Jacques Chirac, riƙon sakainar kashi. Shugaba Chirac dai, ya bukaci taron ya yi shawarwari ne kan samad da wani zaɓi na tafiyad harkokin tattalin arzikin duniya, maimakon tsarin jari-hujja salon Amirka, da ya zamo mizani ga kusan duk ƙasashen rukunin na G-8. Amma shugaba Bush bai ɗau wannan ajandar da muhimmanci ba. Ya bar taron kafin lokaci, ya tafiyarsa zuwa Sharm-el-Sheikh a ƙasar Masar, wai don halartar wani taro kan yankin Gabas Ta Tsakiya. Shekara ɗaya bayan hakan, a lokacin da Amirkan ke karɓar baƙwancin taron a Sea Island, sai aka mayar mata da martani. Mahalarta taron dai sun juya wa shirin da Washington ta gabatar baya, inda take neman a zartad da wani ƙuduri na gabatad da tsarin dimukraɗiyya salon Amirkan a duniyar musulmi. Sauran ƙasashen na ganin Amirkan na son ta yi amfani da su ne wajen cusa manufarta a ƙasashen musulmin. Sabili da haka ne suka yi biris da shawarar.

A shekarar bara kuma, hare-haren ƙunan bakin waken da aka kai a birnin London, su suka dabaibaye taron G-8 ɗin da aka yi a Gleaneagles a Birtaniya. Amma darasin da aka koya daga waɗannan hare-haren su ne, wato ko wane irin salo na ta’addanci na da tushensa ne daga talauci, da rashin ci gaban halin rayuwa a yannkuna daban-daban na duniya. Kai tsaye ne dai, shirin da Tony Blair ya gabatar na yaƙan talauci da kuma yafe wa ƙasashe matalauta basussukansu ya sami cikakken goyon baya.

A taron St.-Petersburg kuma, lamarin ba daban ya kasance ba. Halin yaƙi da aka shiga ciki a yankin Gabas Ta Tsakiya, ya tilasa wa mahalarta taron canza ajandarsu, don su fi mai da hankali kan sabon rikicin. Duk duniya dai ta sa ido ne don ta ji irin bayanan da shugabannin ƙasashe mafi arzikin masana’antun za su yi a kan rikicin da ke ta’azzara a yankin na Gabas Ta Tsakiya. Da dai wannan rikicin bai ɓarke ba, da watakila masharhanta da dama sun sanya alamar tambaya kan dalilin kiran taron ma gaba ɗaya.

A ƙarshen taron na rukunin G-8 dai, duk ƙasashen sun yi kira da murya ɗaya ga abokan hamayyar na Gabas Ta Tsakiya da su tsagaita buɗe wa junansu wuta. Wannan dai wani abu ne da bai taɓa faruwa ba. A karo na farko, Amirka ta sanya hannu kan wani ƙuduri, wanda ke kira ga Isra’ila da ta dakatad da yaƙin da take yi a yankin. A karo na farko kuma, Rasha da Faransa sun yi suka ga ƙungiyoyin Hamas da Hizbulahi tare da yin kira ga sako sojojin Isra’ila da kungiyoyin ke garkuwa da su. Har ila yau dai, a rana ɗaya kawai, ban da kiran da ƙasashen G-8 ɗin suka yi, an kuma cim ma nasarar gabatad da wani shiri na tura jami’an sa ido ƙarƙashin ofishin manzancin samad da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya, don kwantad da ƙurar rikici a yankin.

A nan Jamus dai, ana ganin cewa, sanya hannun da shugaban gwamnatin tarayya Angela Merkel ta yi a kan ƙudurin, wato ya share fagen tura dakarun Jamus ke nan, ƙarƙashin laimar dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniyar, zuwa layain da aka shata tsakanin Isra’ila da Lebanon, idan bukatar yin hakan ta kama.

Abin da za a iya cewa a nan, kuma game da taron na G-8 na wannan shekarar dai shi ne, shugabannin ƙasashen wannan rukunin, ba sa farkawa daga barcin da suke yi, sai bamabamai da rokokin da ke halaka ɗimbin yawan fararen hula, sun tilasa musu yin hakan.