An kammala taro tsakanin Korea Ta Kudu da Ta Arewa kafin lokaci. | Labarai | DW | 13.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala taro tsakanin Korea Ta Kudu da Ta Arewa kafin lokaci.

An kammala wani taron tuntuɓar juna tsakanin ƙasashen Korea Ta Kudu da Ta Arewa kafin lokaci, kuma ba tare da cim ma wata madafa ba, bayan rashin jituwar da ɓangarorin biyu suka samu a kan batun gwajin rokokin da Korea Ta Arewan ta yi a kwanakin bayan nan. Ƙasar Korea Ta Arewan, na zargin maƙwabciyarta ta kudu ne da janyo wargajewar taron. A ganin mahukuntan birnin Pyongyang dai, batun harkokin soji bai shafi tsarin tuntuɓar juna tsakanin ƙasashen biyu ba.

A halin da ake ciki yanzu, Japan, tare da ɗaurin gindin Amirka, na ci gaba da neman Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya sanya wa Korea Ta Arewan takunkumi, saboda gwajin rokokin da ta yi, yayin da ƙasashen Sin da Rasha kuma, suka gabatad da nasu bukatun, waɗanda ba su ƙunshi ɗaukan matakan sanya wa ƙasar takunkumi ba.