AN KAMMALA TARO KAN KASAR AFGHANISTAN A BERLIN | Siyasa | DW | 01.04.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

AN KAMMALA TARO KAN KASAR AFGHANISTAN A BERLIN

An kammala taron kasa da kasa da aka shirya kan Afghanistan a babban birnin tarayya. Batun tsananta matakan tsaro a lokacin zaben da za a yi a kasar a cikin watan Satumba mai zuwa, na cikin muhimman ababan da aka tattauna a gun taron. Gamayyar kasa da kasa kuma, ta dau alkawarin bai wa Afghanistan din taimakon kudi na kimanin dola biliyan 8 da digo 2.

Ministan tsaron Jamus, Peter Struck

Ministan tsaron Jamus, Peter Struck

Duk wanda ya tallafa wa yunkurin da ake yi na farfado da Afghanistan, wato ya kuma lashi takobin yakan ta’addanci ke nan. Da wannan furucin ne dai, ministan tsaron Jamus Peter Struck, ya kammala jawabinsa na rufe taron da aka shafe yini biyu ana shawarwari kan taimakon da gamayyar kasa da kasa za ta bai wa Afghanistan. Babu shakka, ministan na neman wani mukamin kasasru ne na bai daya, na kwatanta dalilin da ya sa kasashe fiye da 50 suka turo wakilansu zuwa Berlin don halartar taron, da kuma daukar alakawarin ba da taimako ga yunkurin da ake yi na sake gina kasar ta Afghanistan.

Akwai dalilai da dama da suka sanya kasashen yin taron kan wannan kasa ta Afghanistan. Na farko dai shi ne: suna sha’awar ganin cewa kasar ta fice daga kangin danniya, da yake-yake da tashe-tashen hankullan da ta yi ta fama da su, ta shiga cikin wani sabon zamani na zaman lafiya karkashin mulkin dimukradiyya. Sai kuma manufar nan ta yakan tadaddanci da suka sanya a gaba, inda suka nanata cewa, gurinsu ne fatattakar `yan ta’addan daga kasar ma gaba daya. Wani dalilin kuma, ya shafi batun habakar kasuwancin miyagun kwayoyi ne a duniya. Afghanistan dai, ita ce kasar da aka fi noman shuke-shuken miyagun kwayoyi a cikinta, a duniya.

Duk kasashen da suka halarci taron dai, na sa ran samun wata fa’ida nan gaba a kasar ta Afghanistan, ko kuma kare maslaharsu a yankin Asiya. Babu shakka, bayan yakin da Afghanistan din ta yi ta fama da shi a cikin fiye da shekaru 20 da suka wuce, da kuma daukin da Amirka ta yi mata, don hambare gwamnatin Taliban, kasar na bukatar duk wani taimakon da za ta samu a halin yanzu.

A taron na Berlin dai, gamayyar kasa da kasa ta dau alkawarin ba da taimakon kudi na kimanin dola biliyan 8 da digo biyu ga yunkurin sake gina wannan kasa. Sai dai, mahukuntan Afghanistan din sun bukaxci fiye da haka. Bisa nasu kiyasin dai, kasar za ta bukaci kimanin dola biliyan 28 ne a cikin shekaru 7 masu zuwa, idan har tana son ta cim ma gurin da ta sanya a gaba.

Masharhanta da yawa ne ke ganin cewa, alkawarin da kasashen Yamma suka dauka, romon baka ne kawai. Saboda a wasu tarukan da aka yi a shekarun baya ma, haka lamarin ya kasance. Ba su ba da kudaden da suka yi ta shelanata cewa za su bayar ba.

Amma duk da haka, mahalarta taron na Berlin, sun bayyana ra‘ayin cewa, an cim ma gagarumin nasara a tattaunawar da aka yi. Gamayyar kasa da kasa ta farga da nauyin da ya rataya a wuyarta game da wannan kasa ta Afghanistan, wadda a halin yanzu, babu abin da aka fi saninta da shi a duniya kamar miyagun kwayoyi, da talauci da kuma wahalhalun da `yan kasar ke fama da su, tun ma kafin hawar karagar mulkin ?asar da `yan kungiyar Taliban suka yi.

 • Kwanan wata 01.04.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvkv
 • Kwanan wata 01.04.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvkv