An kammala taro kan harkokin tsaro a Najeriya | Labarai | DW | 14.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala taro kan harkokin tsaro a Najeriya

Shugaban kasar Faransa François Hollande ya yi kira ga kasashen duniya da su kara ba da taimako ga kasashen Yankin tafkin Chadi a kokarin da suke na samar da tsaro.

Shugaban na Faransa ya yi wannan kira ne ya yin bude babban zaman taron da ya gudana a birnin Abuja na Tarayyar Najeriya kan batun yaki da ta'addancin da kungiyar 'yan ta'adda na Boko Haram inda cikin jawabin na shi yake cewar:

" Boko Haram ita ce kungiyar 'yan ta'adda wadda ta fi kowacce hallaka jama'a a duniya, kuma mu kasar Faransa mun san da haka, ta la'akari da abin da Kungiyar IS ke yi a kasashen Iraki da Siriya, kuma mun yi gaskiyya da muka nuna damuwarmu kan abin da ke wakana a Somaliya da ma Libiya, amma Boko Haram ita ce kan gaba wajen rishin nuna imani."

Shugaban Tarayyar Najeriya dai Muhammadu Buhari ya sanar cewar tallafin da yakamata a samar domin fuskantar wannan matsala da kuma raya , ta kai ta Euro miliyan 960, inda ya ce ta haka ne za a yaki dalillan da ke haddasa samun iri-irin wadannan kungiyoyi na 'yan ta'adda.