1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala shawarwarin kafa babbar gwamnatin kawance a Jamus

November 12, 2005
https://p.dw.com/p/BvLT

Kusan makonni 4 bayan zaben ´yan majalisar dokokin Jamus ta Bundestag, jam´iyun Christian Union da SPD sun kammala shawarwarin kafa gwamnatin kawance tsakaninsu. Shugabannin jam´iyun sun amince da wata yarjejeniyar kulla kawancen wadda a yau asabar za´a bayyana ta a hukumance. Idan har manyan tarukan da jam´iyun CDU da CSU da SPD zasu yi a ranar litinin suka albarkaci yarjejeniyar, to hakan zata share fagen kulla wani kawance na biyu mafi girma a Jamus, wanda kuma zai ba da damar zaben shugabar CDU Angela Merkel a matsayin shugabar gwamnati a ranar 22 ga watan nan na nuwamba. Babban burin gwamnatin dai kamar yadda Christian Union da kuma SPD suka nunar shi ne daukar managartan matakan rage yawan marasa aikin yi a Jamus. Ana fatan wani shirin zuba jari na kudi Euro miliyan dubu 25 zai taimaka a cimma wannan buri. Sassan biyu sun amince su kara kudin haraji akan kayan alatu daga kashi 16 zuwa 19 cikin 100 a farkon shekara ta 2007.