1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala aikin Hajji ba tare da wani hadari ba a Jimarat

January 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuVn
Musulmi kimanin miliyan 3 ne suka gudanar da rukuni na karshe na aikin hajjin banna a kasar Saudiya. Sabbin matakan tsaro da aka gabatar kwanan nan sun taimaka wajen hana aukuwar hadurra kamar yadda aka saba gani a lokutan Hajji a shekarun baya. An girke dubban ´yan sandan Saudiya hade da jiragen sama masu saukar ungulu a yau rana ta karshe ta jifar shaidan a gadar Jimarat dake Mina. A lokacin aikin hajjin bara, akalla alhazai 345 aka tattake har lahira a wani turmitsitsi da ya auku a wurin jifar shaidan.