1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kame yan´adda 14 a Spain

May 28, 2007
https://p.dw.com/p/BuKa

Jami´an yan sanda a Spain sun cafke wasu mutane 14 ,da suke zargin na bawa yan ta´adda horo. An dai kame mutanen ne a birnin Bacelona da kuma Catalonia. Daukar matakin yazo ne bisa umarnin wata karamar kotun kasar na´a gudanar da sintiri a guraren biyu..Wannan dai kamen yazo dai dai ranar da ake gurfanar da yan ta´addan da ake zargi da tashin bama baman nan na birnin Madrid, a shekara ta 2004. Da yawa dai daga cikin mutanen da ake zargi da aikata wannan danyan aiki yan kasar Morocco ne.