An kame ma´aikatan haƙo mai 2 na Phillipes a yankin Niger Delta | Labarai | DW | 20.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kame ma´aikatan haƙo mai 2 na Phillipes a yankin Niger Delta

A ci gaba da garkuwa da ma´aikata haƙo man petur a yankin Niger Delta, na taraya Nigeria, an ƙara capke wasu mutane 2, yan ƙasar Philipines, a ranar yau talata.

Ma´aikatan 2, na aiki tare kampanin haƙar mai na PGS mai cibiyar sa, a ƙasar Nowe.

Ya zuwa yanzu, babu ƙungiyar da ta hito hili, ta bayyana ɗaukar alhakin wannan kamu , duk da cewar a na zargin matasan MEND.

Da farkon wannan shekara zuwa yanzu, wannan ƙungiya ta yi garkuwa da turawa masu aiki a kampanonin haƙo mai kimanin 30.

Hare haren MEND da sauran ƙungiyoyin ƙwatar yancin yankin Niger Delta, ya hadasa raguwar yawan man da Nigeria ke haƙowa ko wace rana da kashi 20 buisa 100, a binda ya kara hauda parashen mai a kasuwanin dunia, ta la´akari da cewa Nigeria ke sahu na 6 ,a kasashe masu arzikin man petur na dunia.