1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama 'yan Boko Haram da yawa

Jami'an tsaro a Najeriya suka ce, izuwa yanzu 'yan Bako Haramun 128 suke hannun su, bayan kamen da suka yi yau a Maiduguri.

default

'Yan sandan kwantar da tarzuma a Najeriya

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama mutane 23 a birnin Maiduguri, waɗanda ake zargin cewa 'yan ƙungiyar Boko Haramun ne. 'Yan sandan suka ce suna zargin ƙungiyar da laifin kai harin ɗauki ɗai-ɗai, wanda ya hallaka mutane da yawa a wasu biranen yankin arewa maso gabacin ƙasar. Jami'an tsaro suka ce izuwa yanzu yawan 'yan ƙungiyar Boko Haramun dake hannunsu, sun kai 128. Yanzu haka dai sojoji suna haɗin gyiwa da 'yan sanda don yin sintiri a birnin na Maiduguri da kewaye. Babban jami'in 'yan sanda a yankin Muhammed Abubakar yace yunƙurin nasu yana samun nasara. 'Yan ƙungiyar Boko Haramun dai sun sake bullowa bayan kusan shekara guda, da aka daina jin ɗuriyarsu. Tun bayan karawa da sojoji bara, abinda ya kai ga hallaka mutane kimanin 700, ciki harda shugaban ƙungiyar Muhammed Yusuf wanda ake zargin 'yan sanda suka yiwa kisan gillah.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal