An kama wasu jami´an zabe a Jamhuriyar Demukiradiyar Kongo | Labarai | DW | 12.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama wasu jami´an zabe a Jamhuriyar Demukiradiyar Kongo

Hukumomi a kasar JDK sun kama jami´an zabe guda 6 da ake zargin su da kokarin juya sakamakon zabukan shugaban kasa da na ´yan majalisar dokoki da aka gudanar a kasar bayan bayan nan. Wani kakakin hukumar zabe ta JDK ya ce an kama mutanen ne a lokacin da suke kokarin canza lissafin kuri´un da aka kidaya. Hakan dai ya zo a lokacin da wasu ´yan takara wadanda a da ma ba zasu kai labari ba, suka yi zargin tabka magudi a zaben wanda ya kasance irinsa na farko a Kongo cikin shekaru fiye da 40. Sakamakon farko da ake samu sun nuna cewa shugaba mai ci Joseph Kabila ke kan gaba da yawan kuri´u to sai dai ba za´a samu cikakken asakamakon zaben ba sai kashen wannan wata na agusta.