1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama wani dan Najeriya a Jamus

'Yan sanda a nan Jamus sun kame wasu mutane biyu daya dan kasar Aljeriya daya kuma dan Najeriya a bisa zarginsu da shirya kai wani harin ta'addanci a cikin kasar. 

An kama mutanen ne a wannan Alhamis a lokacin wani sumame da 'yan sanda 450 suka kai a birnin Göttingen na tsakiyar kasar bayan da suka samu wasu bayanan sirri da ke nuna cewar mutanen wadanda mambobin Kungiyar Musulmi Salafawa ne na shirin kitsa kai wani hari a kasar. 

Mutane kimanin 550 ne masu alaka da Kungiyar Salafawa a Jamus mahukuntan kasar suka jera a jerin sunayen mutanen da ke a matsayin wata babbar barazana a kasar. 

Kasar Jamus wacce sannu a hankali Musulmi masu akidar Salafanci ke yaduwa a cikinta a 'yan shekarun baya bayan nan, ta fuskanci jerin hare-haren ta'addanci wadanda Kungiyar IS ta dauki alhakin kai su.