An kama ministan kudi na kasar Rasha | Labarai | DW | 15.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama ministan kudi na kasar Rasha

Rahotanni daga Rasha na cewa mahukuntan kasar sun kama ministan ma'aikatar kudi ta kasar wato Alexei Oulioukaiev a bisa zargin karbar rasahawa ta kudi miliyan biyu na dalar Amirka.

 

A cikin wata sanarwa da babban kwamitin bincike na kasar ta Rasha ya fitar a wannan Talata, ya ce an kama ministan ne a lokacin wani aikin bincike da babbar hukumar tsaro ta kasar wato FSB ta gudanar inda ta same shi da hannu dumu-dumu da karbar na goro a lokacin bayar da wata kwangilar aikin mai da ya bai wa kamfanin Rosneft da ke aikin mai a kasar ta Rasha a watan Oktoban da ya gabata. 

Kwamitin binciken ya bayyana cewa idan dai har shari'a ta tabbatar da zargin da ake yi wa ministan wanda ke rike da wannan mukami na ma'aikatar kudi tun a shekara ta 2013, to kuwa za a iya yanke masa hukunci na zaman wakafi na shekaru 8 zuwa 15.