1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi 'yan Rohingya da safarar kwayoyi

Abdul-raheem Hassan
May 14, 2018

Jami'an tsaron kasar Bangaladesh sun kai samame kan wasu gungun masu safarar kwayoyin maye, an kuma kame mutane kusan 2,000 da ake zargi.

https://p.dw.com/p/2xi0O
Bangladesch Prozess gegen Ex-Regierungschefin Khaleda Zia
Hoto: DW/M. M. Rahman

Hukumomin kasar ta Bangladesh sun kaddamar da kamen ne a wani mataki na dakile tasirin kasuwancin sinadaran buguwa a kan iyakar kasar, shugaban rundunar yaki da fataucin muggan kwayoyi Benazir Ahmed ya yi kira ga sauran masu safarar kwayoyin da su gaggauta mika kansu.

Tuni dai kotu ta yanke hukunci kan mutane 1,400 da suka shiga hannu wadanda aka samu da safarar kayan maye. Hukumomin sun tabbatar da kame adadin kwayoyin maye miliyon 9 cikin watanni Uku a farkon wannan shekarar. Jami'ai a kasar Bangaledesh dai na zargin 'yan gudun hijiran Rohingya da shigo da wasu kwayoyoin maye cikin kasar.