1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama masu niyar gudanar da ayyukan tarzoma a Jamus

October 2, 2011

An cafke wasu masu tsatsauran ra'ayin addini islama guda hudu a nan birnin Bonn bisa zargin makarkashiyar kai harin ta'addanci a yayin bikin hadewar Jamus ta Yamma da ta Gabas.

https://p.dw.com/p/12kgw
Lokacin da jami'an tsaro suka kai wani ɗan Al-Kaida kotu a KarlsruheHoto: dapd

Jami´an tsaron a nan birnin Bonn na Tarayya Jamus sun cafke wasu mutane guda ukku masu tsatsauran ra´ayin addinin musulunci bisa zargin shirya makarkashiyar kai harin ta´adanci a daidai lokacin da birnin ke shagulgulan cikar shekaru 21 da sake hadewar kasar. Kana a kusa da birnin Frankfurt da ke tsakiyar jamus ma an cafke mutum guda bisa zargin kitsa manakisar harin ta'addanci.

kakakin rundunar 'yan sandar Jamus yace an samu mutanen hudu da wasu sinadarai na hada bam-bamai. Ranar litinin nan ne dai,a fadin tarayyar Jamus baki daya ,ake bikin cika shekaru 21 da samun hadin kai tsakanin Jamus ta gabas da ta yamma. A shekara bana dai birnin Bonn aka dorawa yaunin karbar bikin na kasa baki daya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Usman Shehu Usman