An Kai Sabon Hari a Maiduguri Najeriya | Labarai | DW | 12.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An Kai Sabon Hari a Maiduguri Najeriya

Wasu da ba'a san ko su wanene ba sun ƙona ofishin 'yan sanda da ke Gamboru, a Maiduguri babban birnin Jihar Borno Najeriya

default

'Yan sandan Najeriya

Jami'an tsaro a Najeriya, sun ce waɗansu da ake zargin cewa mambobin ƙungiyar da ta ɗauki alhakin tayar da tarzoma ne a bara, ta ƙona wani ofishin 'yan sanda a arewacin ƙasar.

Wani jami'in 'yan sanda da bai yarda a bayyana sunan sa ba, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa a daren jiya ne, waɗansu da ba'a san ko su wanene ba su kai hari a ofishin 'yan sandan da ke Gamboru a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, wanda har ya kai ga ƙonewar ofishin.

'Yan sanda biyu sun sami mummunar rauni a misayar wutar da aka yi, kuma a yanzu haka suna kwance a asibiti, a yayin da har yanzu baa san inda wasu biyu daga cikin 'yan sandan suke ba.

Jami'in ya ƙara bayyana cewa grenati mai ƙirar gida ne aka harin da shi, kuma suna zargin ƙungiyar Boko Haram da aikata wannan ta'asar.

Kakakin 'yan sanda Emmanuel Ojukwu, wanda ya ce an gaya masa batun harin da makaman da aka yi amfani da su, ya ce ba ƙungiyar Boko Haram kaɗai ake zargi da aikata wannan ta'asar ba a yanzu, sai an kammala bincike.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Umaru Aliyu