An kai sabbin hare-hare a yankin Niger Delta a Najeriya | Labarai | DW | 20.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai sabbin hare-hare a yankin Niger Delta a Najeriya

´Yan bindiga daɗi a Najeriya sun kai hari kan wata cibiyar haƙar mai dake yankin Okrika a jihar Rivers. Rahotanni sun ce tsagerun, sunyi garkuwa da wasu ´yan Filifino 18 na wani ɗan gajeren lokaci. Kwamandan rundunar sojin kiyaye zaman lafiya a yankin, Major Sagir Musa ya ce tuni aka sako ´yan Filifinon. Dukkanninsu a cewar Major Sagir na cikin ƙoshin lafiya. Bayanai sun ce bayan wani artabu na wani ɗan lokaci, sojin na Najeriya sun fatattaki tsagerun daga wannan yanki. Tsagerun sun kai harin ne da zummar ƙwace madafun ikon tafiyar da harkokin haƙar man ne a yankin na Okrika. Yankin Niger Delta, yankine da ya yi ƙaurin suna a Najeriya, wajen fuskantar tashe-tashen hankula da kuma rikice-rikicen tsageru.