1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai karar wasu kasashen Turai kan yanayi

Gazali Abdou Tasawa
May 17, 2018

Hukumar zartarwa ta Tarayyar Turai ta kai karar wasu kasashe shida na Turai da suka hada wadanda Faransa da Jamus a gaban kotun Tarayyar Turai a bisa rashin mutunta matakin tsarkake yanayi. 

https://p.dw.com/p/2xtH8
03 BG Das erwartet uns im Juli
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Scholz

Sauran kasashen da matakin hukumar zartarwar Turan ya shafa sun hada da Italiya da Hangari da Rumaniya da Birtaniya wadanda dukkaninsu hukumar ke zarginsu da kin mutunta dokar da ta tanadi rage fitar da gurbataccen hayakin da motoci da kamfanoni da makamantansu ke fitarwa musamman a manyan biranen kasashensu.

Wani bincike da hukumar kula da muhalli ta Tarayyar Turai ta gudanar, ya nunar da cewa gurbatacciyar Iskar da ke yaduwa da kuma jama'a ke shaka na zamo dalilin mutuwar mutane kimanin dubu 400 a shekara daga ciki dubu 66 a Jamus dubu 60 a Italiya, dubu 35 a Faransa.