An kai harin kan kungiyoyin agaji guda biyu a Darfur | Labarai | DW | 20.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai harin kan kungiyoyin agaji guda biyu a Darfur

Bayan wani hari da aka kai kan wasu kungiyoyin ba da agaji guda biyu a yankin Darfur, an sake kwashe ma´aikatan agaji su kimanin 70 daga wannan yanki mai fama da rikici dake yammacin Sudan. Wata sanarwa da kungiyoyin suka bayar ta ce wasu ´yan bindiga su kimanin 20 sun kutsa harbar kungiyoyin inda suka yi awon gaba da motoci 12. Kungiyar Oxfam ta Birtaniya da takwararta ta Faransa wato Action Contre la farm suna kula da ´yan gudun hijira sama da dubu 130 a yankin na Darfur. Harin dai shi nne mafi muni da aka taba kaiwa wasu kungiyoyin agaji a wannan yanki. A cikin wannan watan kadai kungiyoyin sun kwashe ma´aikatansu fiye da 400 saboda tashe tashen hankulan dake kara yin muni a Darfur.