An kai hari kan masallacin Shia′a a Samarra | Labarai | DW | 13.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hari kan masallacin Shia'a a Samarra

Rahotanni dake shigowa daga Iraki sunce an kai wani harin bam akan masallacin Askari na yan shi’a dake birnin Samarra.

Wadanda suka ganewa idanunsu sunce hasumiyoyi biyu na masallacin sun lalace cikin wannan hari.

A shekarar data gabata an kai hari kann wannan masallaci wanda ya janyo tashe tashen hankula na darika a Iraqi da suka haddasa hasarar rayukan dubun dubatar jamaar kasar ta Iraki.