An kai hari kan kotun gudanarwa a Turkiya | Labarai | DW | 17.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hari kan kotun gudanarwa a Turkiya

An kashe wani alkali sannan aka yiwa abokanen aikin sa su 4 rauni a wani hari da aka kai kan babbar kotun gudanarwa dake birnin Ankara a can kasar Turkiya. ´Yan sanda sun cafke wanda ya kai harin. Kafofin yada labaru sun labarto cewa mutumin da ya kai harin wani mai tsattsauran ra´ayin addinin Islama ne wanda ya taba aiki a mastayin lauya a cikin kasar. Sau da yawa dai masu kishin Islama kan kaiwa kotun gudanarwar hare hare musamman saboda hukunci da ta ke yankewa na goyon bayan tsarin rayuwa ta ´yan kasashen yamma kamar haramta daura dan kwali. Shugaban kasa Ahmet Necdet Sezer ya ce tsarin shari´ar kasar ta Turkiya ba zai saduda ga bukatun masu kishin addini ba.