1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari gidan shugaban Palasdinawa

June 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuJH

Wasu yan bindiga dadi sun bude wuta kann mai uwa da wabi, a gidan faraministan yankin Palasdinawa, Ismail Haniyya.Ya zuwa yanzu dai babu bayanin rasa rai ko kuma jikkata. Al´amarin dai ya faru ne kwana daya, bayan wani dauki ba dadi da akayi a tsakanin kungiyyar Hamas da kuma yan jam´iyyar Fatah, da hakan yayi sular mutuwar mutan 4 da kuma jikkatar wasu 30. Faraministan na Palasdinawa dai ya kasance jagoran kungiyyar ta Hamas, kungiyya da ake mata kallon ta yan ta´adda ce.