1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari a gaban fadar sarkin Saudiyya

Gazali Abdou Tasawa
October 8, 2017

Wani dan bindiga ya kai hari tare da halaka jami'an tsaro biyu na fadar sarkin Saudiyya a birnin Jeddah, wasu mutanen uku kuma sun jikkata. 

https://p.dw.com/p/2lSFg
Saudi-Arabien Konigspalast in Dschidda
Hoto: Imago/Alexander Shcherbak

Rahotanni daga kasar Saudiyya na cewa a jiya Asabar wani mutum dauke da bindiga ya kai hari tare da halaka jami'an tsaro biyu a fadar sarkin Saudiyyar a birnin Jeddah, wasu mutanen uku kuma suka jikkata. 

Kamfanin dillancin labaran kasar ta Saudiyya SPA  ya ruwaito ministan cikin gida na kasar na cewa maharin ya kai farmakin ne dauke da bindiga kirar Kalashnikov da gurneti guda uku inda ya bude wuta tun a bakin kofar fadar tare da kashe biyu daga cikin askarawan da ke gadi, kafin daga karshe a yi nasarar bindige shi.