An kafa wata Ƙungiya ta kawo ala′adun nahiyar Turai a ƙarƙashin laima ɗaya. | Zamantakewa | DW | 25.07.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

An kafa wata Ƙungiya ta kawo ala'adun nahiyar Turai a ƙarƙashin laima ɗaya.

Shirin na wannan makon, zai dubi harkokin al’adu ne a nan nahiyar Turai, inda kafofi da dama ke tambayar wai shin da akwai wata al’ada kuwa da za a iya kira ta Turai a halin yanzu? Da wane mizani ne za a iya auna kasancewar mutum ɗan nahiyar Turai?

Masu zanga-zanga don neman inganta harkokin al'adu a Faransa da kuma Turai

Masu zanga-zanga don neman inganta harkokin al'adu a Faransa da kuma Turai

Waɗannan dai na cikin jigogin da a halin yanzu, masharhanta da dama na nahiyar Turai ke ta muhawara da rubuce-rubuce a kansu. Jama’a da yawa dai na ganin cewa, kasancewa ɗan nahiyar Turai, ba shi ne cim ma daidaito kan samad da kuɗin bai ɗaya na Euro ba ko kuma samad da dokokin da za su aiki a duk ƙasashen nahiyar ba.

Ma’aikatar harkokin wajen Jamus ma ta shiga cikin wannan muhawarar, inda ta gayyato wakilan kafofin al’adu, da ministocin harkokin waje da na al’adu daga ƙasashe 24 na Turai zuwa birnin Berlin, don tattaunawa kan waɗannan batutuwan. Sakamakon da aka samu a taron dai shi ne: an yarje kan cewar ya kamata a kafa wata Ƙungiya, wadda za ta zamo laima ko kuma uwa uban duk ƙungiyoyin al’adu na ƙasashen Ƙungiyar Haɗin Kan Turai.

Cibiyar al’adun nahiyar Turai da ke birnin Berlin ta ƙunshi

ƙungiyoyin al’adu 14 da wasu ƙananan ƙungiyoyi da take ma’ammala da su. Akwai dai irin waɗannan ƙungiyoyin a birane Paris, da Amsterdam, da Brussels sa kuma Vienna. Tun da daɗewa ne dai suke aiki da ƙungiyoyin ƙasashensu, kwatankwacin irin wanda za a yi yanzu a nahiyar Turai gaba ɗaya. Joana Kliszek, daraktan cibiyar al’adun ƙasar Poland da ke birnin Berlin, wadda ita ma ta halarci taron a babban birnin na tarayya, ta bayyana cewa, burin da ake son cim ma dai shi ne:-

„Girmama al’adun ƙasar mutum na asali da kuma al’adun ƙasar da yake zaune a ciki a halin yanzu, don samun daidaito na bai ɗaya tsakanin duk ƙasashen nahiyar Turan, abin da ma zai iya zamowa misali ga duk duniya baki ɗaya. Sai an cim ma haka ne, za a iya yin batun al’ada ko kuma al’adun nahiyar Turai, inda wato aka cim ma nasarar haɗe duk al’adun ƙarƙashin laima ɗaya. Duk da hakan, ko wace ƙasa za ta kasance yadda take da halayyarta, ba tare da yin asarar alamun da suka bambanta ta da sauran ƙasashe ba.“

Wasu masharhantan dai na sanya alamun tambayoyi kan wannan shirin. Ta yaya wata ƙasa za ta iya kare al’adunta, sa’annan a lokaci ɗaya kuma ta rungumi wata al’ada wai ta Turai gaba ɗaya? Ta yaya ma za a iya tafiyad da shirin al’ada ta bai ɗaya, inda ake da harsuna daban-daban? Wannan nau’in masharhantan dai na ganin cewa, ba wajen sadaswa kawai yin amfani da harsuna ke da ma’ana ba. Ko wane harshe na bayyana halin rayuwar masu yin amfani da shi, da yadda suke hangen duniya, da kuma zamantakewa a cikinta.

A ɗaya ɓangaren kuma, magoya bayan shirin na bayyana ra’ayoyin cewa, ai wannan bambancin harsuna da kuma yawan al’adu ne abin da ke alamta al’adar ta Turai gaba ɗaya. Jean Claude Crespy, na Cibiyar Al’adun Faransa, na ɗaya daga cikin magoya bayan shirin. A ganinsa dai:-

„Abin da ke alamta mu, wato yana da wuyar ganewa. Saboda ya dogara ne kan tuntuɓar juna. Idan bajamushe ya sadu da wani bajamushe, ba zai taɓa tambayar kansa ko akwai wani abin da ya bambanta su ba. Amma idan bajamushe ya sadu da bafaranshe ko ɗan ƙasar Poland, to dole ne sai ya yi tuanin asalin inda ya fito da kuma abin da yake da shi na bai ɗaya da mutumin da ya sadu da shi, ko kuma abin da ya bambanta su. Ina ganin wannan shi abin da ke da wuyar ganewa wajen bayyana asalinmu.“

Ban da kasancewarsu daga nahiya ɗaya, abin da ke haɗa Turawa waje ɗaya, duk da bambance- bambancensu, shi ne wasu ƙa’idodji na bai ɗaya da dukkansu suka amince da su, waɗanda kuma ke ƙunshe cikin kundin tsarin tafiyad harkokin gamayyar Turan, inji Teresa Indjein ta cibiyar al’adun ƙasar Austriya. A nata ganin dai, kare hakkin ɗan Adam, da kau da wariyar jinsi tsakanin namiji da mace, wato jigajigai ne da ake samunsu a cikin duk al’adu na duniya. Amma bai kamata a mai da su mallakar wani addini, ko kuma a yi ƙoƙarin yaɗa su ta hanyar wani addini guda ɗaya tak kawai ba. Abin da zai fi ma’ana shi ne, a sami wani dandalin tuntuɓar juna, inda kowa zai iya bayyana ra’ayinsa da kuma kare matsayinsa, ba tare da nuna ƙyama ga matsayin sauran ba. Kamar dai yadda ta bayyanar:-

„Tsarin da muke da shi yanzu, tsari ne ingantacce, wanda ke ba mu damar cuɗanya da baƙi daga wajen nahiyar Turai. Kusantar juna dai wani aba ce da ya kamata mu yi hankali da ita.“

A nan dai sabuwar Cibiyar al’adun ta nahiyar Turai da aka kafa, za ta iya taka muhimmiyar rawar gani, inji Eleftherios Ikonomu daga ƙasar Girka, wanda shi ne kuma shugaban gamayyar cibiyoyin al’adun nahiyar Turai da ke da mazauninta a birninn Berlin:-

„Burinmu ne dai, mu dinga tuntuɓar juna tsakanin cibiyoyin al’adu na nan nahiyar Turai. Daga bisani ne kuma, za mu iya bayyana fa’idar da muka samu a wannan huskar, a wasu yankuna kamarsu Asiya, da Afirka da Latinamirka. A waɗannan yankunan ma, muna da rassan cibiyoyin al’adun nahiyar Turai kamar dai su Goethe Institut ta Jamus, da Institut Francais ta Faransa, da Istituto Italiano di Cultura ta Italiya da cibiyar al’adu ta ƙasar Hungary, waɗanda suke aikin haɗin gwiwa da juna.“

Don inganta wannan aikin a huskar al’adu a cikin nahiyar Turan da kuma wajenta ne aka ƙiƙiro wannan cibiyar mai suna EUNIC a taƙaice, wadda za ta kasance uwa uban duk cibiyoyin al’adu na Turai gaba ɗaya. A cikin shekaru biyu masu zuwa dai, jigogin da ta sanya a gaba ne tuntuɓar juna tsakanin al’adu daban-daban, ala’adu da maƙaurata da kuma yin amfani da jam’in harsuna.

 • Kwanan wata 25.07.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvTQ
 • Kwanan wata 25.07.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvTQ