1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AN KAFA SABUWAR GWAMNATI A LEBANON

Zainab A Mohammed.April 19, 2005

Bisa dukkan alamu an kusan gano bakin zaren warware rikice rikicen siyasa daya jima yana addaban Lebanon,sakamakon sanarda kafa gwamnatin hadin kan kasa ayau.

https://p.dw.com/p/BvcP
Beirut,fadar gwamnatin Lebanon.
Beirut,fadar gwamnatin Lebanon.Hoto: laif/Sasse

Bayan an dauki sama da makonni shida ana kai ruwa rana dangane yiwuwan gudanar da zaben kasa a watan Mayu a kasar Lebanon,ayau ne Prime ministaNajib Mikati ya sanar da kafa sabuwara gwamnatin hadin gwiwa ,tare da sanrda cewa zai gaggauta koran dukkan manyan jamian tsaro dake neman cigaba da kasancewar Syria a cikin kasar ta Lebanon.

Wannan sanarwa a yau dai na nuna alamun cewa zaa cimma gudanarda zaben yan majalisar dokokin kasar da aka tsara gudanarwa a watan Mayu dangane da bukatun hukumomin ketare da kuma yan adawa a hannu guda.

Mikati yace sabuwar gwanmnatin ta kunshi minisrtoci dai dai har 14,wadanda bazasuyi takara a zaben mai gabatowa ba.

Ayanzu haka dai wannan sabuwar gwamnati nada kwanaki 10 kachal cikin wanda cimma goyon bayan yan majalisa ,tare da gabatar da bukatunta a gaban majalisar dokoki ,idan har zaa gudanar da wannan zabe kafin waadin yan majalisar na yanzu ya cika ranar 31 ga wata mayu mai tsayawa.

A makon daya gabata nedai aka zabi Prime minista Mikati ,inda ba zata ya samu goyon bayan masu adawa da kasancewar Syria a wannan kasa ,bayan gazawa da premier mai barin gadio Omar Karami yayi wajen kafa sabuwara gwamnati.

Sabon Prime ministan yace a lokacin dayake dan majali ya nemi a sauke jamian tsaro dake marawa cigaba da kasancewar Syria cikin Lebanon daga mukamansu.Yace a matsayinshi na jagoran wannan sabuwar gwamnati zai cigaba da yakin neman cimma burinsa a gaban majalisar zartarwa,inda yayi fatan cewa zai cimma nasara.

Kasar Lebanon dai ta kasance cikin rikice rikicen siyasa ba tare da gwamnati ba ,tun a bayan kisan gilla da akayi wa tsohon Prime minista Rafik al-Hariria ranar 28 ga watan Febrairu,kisanda Lebanawan suka zargi Syria da aikatawa.

Rahotannin hukumar binciken musabbabin kisan Hariri daga majalisar dunkin duniya,na nuni dacewa zai kasan ce abu mawuyaci a cimma tudun dafawa wajen binciken ,idan har manyan jamian tsaron suka cigaba da kasancewa kann karagar mulki.

A yanzu haka dai Syria ta janye kusan dukkan dakarunta daga Lebanon,bayan kasancewarsu a wannan kasa na tsawon shekaru 29,bayan gudurin da aka cimma a majalisar dunkin duniya.

A ranar 14 ga watan Febrairun daya gabata nedai Tsohon Prime minista Rafiq Hariri ya gamu da ajalinsa ta hanyar fashewan Bomb a birnin Beirut,wanda ya jasgoranci tashe tashen hankula a sassa dabab daban na Lebanon ,wanda kuma ya tilasta Syria kawo karshen kakagida da dakarunta sukayi wa kasar kusan shekaru 30 da suka gabata.Duk da kusantakar dangantakarsa da Gwamnatin Syria,Mikati ya samu goyon bayan yan adawa,bayan alkawarinsa na biya wasu daga cikin bukatunsu,musamman na gudanar da zaben kasa tare da koran manyan jamian tsaro saboda halin ko oho da suka nuna dangane kisan gilaan tsohon prime minista Hariri.

Wannan sabuwar gwamnati ta samu kafuwa a yau ne bayan Prime minister mai barin gado kuma mai marawa Syria baya na cigaba da kasancewa a kasar Omar Karameh yayi murabus sau biyu cikin tsukin makonni 6,inda Lebanon ta kasance ba tare da gwamnati ba na tsawon makkonni shida,wanda kuma ke baraza wa yiwuwan gudanar da zaben watan mayu.

Bugu da kari Miqati yace sabuwar gwamnatin kasar zata sa fifiko wajen kalubalantar harkokin tattalin arziki,tare da kare darajar kudin wannan kasa dake rataye da bashin Dala Billion 34.