1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa gwamnatin gamin gambiza a Burundi

Hauwa Abubakar AjejeSeptember 1, 2005

Shugaba Nkurunziza na Burundi ya kafa sabuwar majalisar gudanarwa da ta hada dukkan bangarorin kasar

https://p.dw.com/p/Bva2
Shugaba Pierre Nkurunziza na Burundi
Shugaba Pierre Nkurunziza na BurundiHoto: AP

Tsohon shugaban yan tawayen Hutu kuma sabon shugaban kasar Burundi,Pierre Nkurunziza ya nada sabbin ministoci ashirin,yana mai baiwa yan kabilar Hutu kashi sittin cikin dari,yan kabilar Tutsi kuma kashi arbain cikin dari na matsayoyin,bisa sabon kundin mulkin kasar.

Goma sha biyu daga cikin ministocin yan tsohuwar kungiyarsa ta tawaye ne wato FDD,kodayake hakan bai gamsar da wasu yan kabilar hutu ba wadanda a cewar Leonce Ngundakuman shugaban jamiyar FRODEBU da tayi mulkin kasar a baya, jamiyarsa tayi tsammanin samun kujeru a maaikatu biyar amma sai ga shi sun kare da kujeru uku kacal.

A hira da sabon Ministan yada labarai da aka nada cikin sabbin ministocin, Ramadhani Karenga kuma tsohon maaikacin Rediyo Deutsche Welle, yace ya gamsu da yadda gwamnatin ta raba wadannan mukamai.

Yace ba ma baiwa yan Hutu kashi 60 yan Tutsi kuma kashi 40 kadai suka yi maraba da shi ba,har ma da baiwa mata da dama mukaman ministoci cikin wannan gwamnati wadda yace gwamnatin ta bi tsarin yarjejeniyar da aka cimmawa ne, haka kuma gwmnatin ta baiwa musulmi biyu wato shi kansa a matsayin ministan yada labarai da kuma ministan ilmi.

kafin sanarda sabuwar gwamnati Nkurunziza ya nada mataimakansa guda biyu a ranar litinin da ta gabata,Martin Nduwimana dan kabilar Tutsi da kuma Alice Nzomukanda daga kabilar Hutu.

Shugaba Nkurunziza ya kuma baiwa Antoinette Batumbwira yar kabilar Tutsi kujerar maaikatar harkokin waje,wadda take daya daga cikin mata bakwai da yana ministoci.

Baiwa mata kashi daya bisa uku a majalisar ministocin ya burge yar kasuwa Jacqline Hatungimana wadda tace baiwa mata matsayi a gwamnati zasu matukar kawo gyara a cikin kasar saboda a cewarta mata basu kula da batun banbancin kabila ba,zasu yi mulki ne a matayinsu na uwaye.

Zaben shugaba Nkurunziza dan shekaru 40 da akayi ranar jumaa da ta gabata ya tabbatar wani abin tarihi ne ga shirin zaman lafiyar kasar da aka rattaba hannu akai a shekara ta 2002 wadda ta kawo karshen yakin basasa na shekaru 12 tsakanin yan tawaye na mafiya rinjayen kabilar Hutu da kuma yan tsirarun kabilar Tutsi da sukayi mulkin kasar na mafi yawan shekaru bayan samun yancin kasar a 1962.

Shugabannin kasashen Afrika sunyi maraba da wannan ci gaba da aka samu a kasar Burundi wadda suka ce hakan wani misali ne cewa Afrika zata iya magance matsalolinta da kanta.

Ga sabuwar majalisar gudanarwar ta gwamnatin shugaba Nkurunziza,babban kalubale da ke gabansu yanzu shine sake farfado da tattling arzikin kasar daya tabarbare,da samarda hanyoyin sasanta alummar kasar da suka dade suna gaba da juna tare kuma kawo karshen burbushin kungiyoyin tawaye da suka saura a kasar.

Nkurunziza shine shugaban kasa na biyu dan kabilar Hutu da aka taba zaba a tarihin kasar Burundi bayan kashe shugaba Melchior Ndadaye da yan Tutsi sukayi watanni kadan bayan zabensa a 1993.