An kafa dokar ta baci Fiji | Labarai | DW | 06.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kafa dokar ta baci Fiji

Shugaban mulkin soja na tsibirin Fiji ya kafa dokar ta baci a kasar,tare da rushe majalisar dokokin kasar.

Hakazalika komanda Frank Bainimarama ya rantsarda firaministan rikon kwarya tare da korar babban jamiin yan sandan Fiji,bayan ya ki bin umurni da sabuwar gwamnatin mulkin sojin ta bashi.

Bainimarama ya fadawa taron manema labarai cewa ya rushe majalisar dokin ne bisa shawarar da sabon firaministan ya bayar saboda ganin cewa jamian tsohuwar gwamnatin ba zasu bada hadin kansu ga sojojin ba.

A halinda ake ciki kuma sojoji dauke da makami sun fitar da firaminista da aka sauke Laisenia Qarase daga babban birnin kasar Suva yayinda suka fara tsare wadanda suke adawa da juyin mulki da akayi